Connect with us

News

Farashin Fetur Na Zuwa Ne Yadda Kasuwa Ta Kasance  – Kamfanin NNPC

Published

on

download (3)

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce man  fetur da kansa ne zai nemawa kansa farashi a kasuwa.

Advertisement

A wata tattaunawa da aka yi da mataimakin shugaban kamfanin na ƙasa Mista Adedapo Segun, ya ce kundin tsarin mulki bai ƙayyade waɗanda za su tsayar da farashin man fetur ba.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shattima Ya Gana Da Shuwagabannin NNPCL Kan Tsadar Mai Fetur

A cewarsa, saahe na 205 da ya kafa kamfanin, ya bashi damar sakin fetur don nemawa kansa farashi a kasuwa.

Advertisement

Ya ƙara da cewa dangane da tsadarsa da mutane ke kokawa, batu ne da ya shafi chanjin kuɗaɗe.

Amma ya ce su na ƙoƙarin su da dilallan man na ƙasa don ganin an magance karancinsa.

Advertisement

Kuma ya sake tabbatarwa da ƴan Najeriya cewar, nan da kwana ƙalilan za a kawo ƙarshen matsalar ƙarancin man baki ɗaya.

A cewar kamfanin, a halin yanzu man fetur na nemawa kansa farashi ne a kasuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending