Connect with us

News

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shattima Ya Gana Da Shuwagabannin NNPCL Kan Tsadar Mai Fetur

Published

on

1725564086219

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya gayyaci karamin ministan albarkatun Man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, da Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, zuwa Aso Rock.

 

Advertisement

Taron wanda ya sami halartar  mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu da mataimaki na musamman ga Shugaban Bola Tinubu  Kan harkokin yada labarai Abdul,az iz Abdul,aziz wanda hakan baya rasa nasaba da karin farashin Man Fetur.

 

Advertisement

Haka kuma a taron akwai wasu jami’an gwamnati daga ofishin mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima.

 

Advertisement

Karin farashin man fetur na baya-bayan nan ya sa farashin sufuri ya tashi sama da kashi 50 a manyan biranen Nijeriya.

 

Advertisement

Sabon karin farashin, wanda Kamfanin (NNPCL) ya aiwatar, ya tashi daga N855 zuwa N897 kowace lita, ya danganta da wurin da ake ciki, daga N568-N617 a baya.

 

Advertisement

‘Yan kasuwa masu zaman kansu sun maida farashin su zuwa tsakanin N930 zuwa N1,200 kowace litar man fetur

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending