Connect with us

News

Mutane 48 Sun Mutu, Shanu 50 Sun Babbake Kurmus Yayin Da Tankar Mai Ta Fashe

Published

on

images 56 600x375

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Wani Ibtila’i da ya afku a ranar Lahadi yayin da mutane 48 suka mutu sakamakon fashewar wata tankar man fetur da ta afku a hanyar Bida-Agaie-Lapai- a jihar Neja ta arewa ta tsakiyar Najeriya.

Advertisement

Abdullah- Baba-Arah, Darakta-janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Neja (NEMA) ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Minna, babban birnin jihar ranar Lahadi.

Mun Samu Nasarori Daga Fara Gudanar Da Aikin Mu Zuwa Yau. Wajen Daƙile Faɗan Daba Da Ƙwacen Waya — KOSSAP

Ya ce hukumar ta samu rahoton wata mummunar fashewar tankar mai da ta afku a ranar Lahadi da misalin karfe 12:30 na safe a kan babbar hanyar Bida-Agaie-Lapai.

Advertisement

A cewarsa, wurin da Ibtila’in ya afku na da nisan kilomita biyu daga ƙauyen Dendo da ke karamar hukumar Agaie a jihar.

Ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da wata tankar mai dauke da mai (PMS) ta yi karo da wata tirela da ke dauke da matafiya da shanu daga Wudil jihar Kano a kan hanyar Legas.

Advertisement

Baba-Arah ya ce wasu motoci guda biyu, wata babbar mota da wata motar daukar kaya suma abin ya ritsa da su cikin lamarin.

Ya bayyana cewa an tabbatar da mutuwar mutane sama da 30, tare da babbakewar shanu sama da 50 suka rasa rayukansu.

Advertisement

 

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending