Connect with us

News

Rundunar Ƴan Sanda Sun Yi Nasarar Kama Mutum Biyu Masu Kera Bindigar AK47 A Bauchi

Published

on

Rundunar Ƴan Sanda Sun Yi Nasarar Kama Mutum Biyu Masu Kera Bindigar AK47 A Bauchi

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta yi nasarar kama wasu mutane biyu dauke da kayan hadin bindigar kirar AK47 da alburusai a karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar.

Advertisement

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Ahmed Wakil Shi ne ya bayyana hakan a yau Alhamis a wani taron manema labarai da ya gudana a Bauchi.

Aƙalla Mutum 67 Ne Suka Kamu Da Cutar Kyandar Biri A Najeriya –Hukumar  NCDC

Wakil ya ce an kama wadanda ake zargin ne a Kasuwar Boto da ke karamar Hukumar Tafawa Balewa, biyo bayan wani rahoton sirri da sashin yaki da masu garkuwa da mutane suka samu.

Advertisement

WIKKI TIMES ta ruwaito cewa wadanda aka kama sun taso ne daga jihar Filato domin su sayar da bindigar wanda suka yi mata kuɗi Naira 580,000,” Wakil ya bayyana.

Ya kuma ƙara da cewa waɗanda ake zargin za su gurfana gaban Kotu idan an kammala bincike

Advertisement

A nasa martanin kwamishinan ‘yan sanda (CP), Auwal Musa, ya sha Alwashin kamo duk waɗanda aka ji labarin suna kera waɗannan kayayyaki.

“Hukumar yan sanda ta himmatu sosai wajen ganin ta kawar da muggan makamai a jihar, kuma muna bukatar yan kasa da su yi kokari wajen ba da hadin kai,” inji shi.

Advertisement

Rundunar yan sanda ta cigaba da cewa kamen wani muhimmin ci gaba ne a kokarin da jami’ai ke yi na yaki da ta’ammali da makamai a jihar.

Haka kuma rundunar ta baiwa jama’a tabbacin cewa ‘yan sanda suna nan suna iya bakin kokarin su wajen tabbatar da tsaro

Advertisement

(NAN)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending