News
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya Kai Ziyarar Jaje Kasuwar Kwari
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai ziyarar jajantawa Yan kasuwar Kantin Jim kadan da dawowarsa daga ziyarar aiki da yaje Abuja.
Dubun dubatar Masoya da magoya baya ne sukayi cincirundo domin raka mai Martaba Sarkin kasuwar ta Kantin kwari.
Akwai Yuwuwar NNPC Ya Sake Fitar Da Farashin Man Fetur A Najeriya
Da yake jajantawa wadanda suka gamu da ibtila’in gobarar, Sakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi addu’ar Allah ya mayar da asarar da akayi a kasuwar tareda addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar hakan anan gaba.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma godewa Jami’an Hukumar kashe gobara ta jihar Kano da Jami’an tsaro da Kungiyar Yan kasuwar da dai daikun al’uma bisa yadda suka bada dugunmawa wajan tabbatar da kashe gobarar.
Sarkin daga nan sai ya bukaci Yan kasuwa da sauran al’uma su cigaba dayin addu’oi domin kiyayewar afkuwar irin wannan ibtila’i tareda neman samun sassaucin al’amura na rayuwar yau da kullum.
Mai Martaba Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yakai ziyarar aiki ne babban Birnin Tarayya Abuja tareda halartar wasu tarurruka, inda daga dawowar sa ne ya zarce domin yin jaje ga Yan kasuwar.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
