News
Tsarin Karɓa-karɓa Babban Koma Baya Ne A Najeriya —Farfesa Kamilu Sani Fagge
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Masana harkokin siyasa irinsu Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin Kimiyyar siyasa ne daga Jami’ar Bayero ya ce tsarin karɓa-karɓa babban koma baya ne a najeriya.
Hakan bukatace kawai irin ta siyasa bawai cigaban Yan Najeriya ko Kuma cigaban Dimukuradiyya ba.
Akwai Yuwuwar NNPC Ya Sake Fitar Da Farashin Man Fetur A Najeriya
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci a yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar na Alif 1999 kwas-kwarima, ta yadda za a rinƙa gudanar da gwamnatin karɓa-karɓa tsakanin shiyyoyi shida da ake da su a ƙasar.
Atiku wanda shine ya yi wa babbar jam’iyar adawa ta ƙasa PDP takarar shugabancin ƙasa a zaɓen da aka yi a shekarar da ta gabata, ya kuma buƙuci ai gyaran ta yadda zai zama tenuwa Daya Mai dauke da shekaru shida Shugaban kasa yake da damar yi me makon tenuwa biyu mai dake duke da shekaru 8.
A cewarsa, hakan zai kara inganta sauyi a sha’anin dimukaradiya da aka kwashe sama da shekaru 25 ana bin tafarkinta a ƙasar.
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce mayar da wa’adin shugaban ƙasa ya zama guda ɗaya na shekara shida zai iya haifar da halin ko-in-kula ga talakawa.
shugabancin karba -karba ba zai iya fitar da kasar nan daga cikin matsalolin da take fuskanta ba. Inji Farfesa Kamilu
Ya ce, alhakin zabar shugaba na gari na wuyan yan Najeriya, ko da kuwa daga bangaren Kudu yake ko Arewa ko kuma banbancin jam’iyya.
Haka zalika ya ƙara da cewa yadda wa’adin shugaban ƙasar yake a yanzu shi ne ya fi dacewa da dimokuraɗiyya domin hakan ne zai tabbatar da cewa shugabanni za su yi wa talakawa aiki.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya miƙa buƙatarsa a wani saƙo da ya aike wa mataimakin shugaban majalisar dattawa, kuma shugaban kwamitin Yiwa kundin tsarin mulkin ƙasar kwas-kwarima senator Barau Jibril Maliya
Idan dai ba a manta ba, majalisun Najeriya sun fara zama don yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999 gyaran fuska, wanda zai shafi gwamnatin karɓa-karɓa da cin gashin kan ƙananan hukumomi da ƙirkirar wasu sabbin jihohi da komawa tsarin gwamnatin shiya shiya da dai sauransu
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
