News
Baza Mu Dena Gwagwarmaya Ba Har Sai Najeriya Ta Samu Gyara —Kwamared Auwal Usman Awareness.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Daraktan ƙungiyar wayar da kan jama’a da kare haƙƙin ɗan adam da tallafawa mabuƙata ta Awareness for Human Right and Charity Foundation, Kwamared Auwal Usman, yace da buƙatar gwamnatin Najeriya ta san matsanancin halin da ƴan ƙasar ke ciki.
Kwamared Auwal ya bayyana hakane ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa da JARIDAR INDA RANKA a safiyar wannan rana, inda yace Mulkin demokradiyya da ake yi a wanann ƙasa kamar bashi da amfani ne kasancewar ƴan ƙasa suna cikin wani hali.
Babban Hafsan Sojoji Janar Lagbaja Na Nan Da Ransa – Rundunar Sojin Najeriya
Ya kuma ce da bukatar manyan ƙasar nan da masu kudi harma da masu faɗa aji a wanan ƙasa da su jawo hankalin gwamantin Najeriya dan muddin aka ci gaba da tafiya a haka to tabbas Najeriya ba zata daga halin da take ciki ba.
Ya kuma ce ya kamata gwamnatin Najeriya da ta jihohi da su yi ƙoƙari wajen samarwa da matasa aikin yi kasancewar sune ƙashin bayan kowacce al’umma domin samarwa da matasan aikin yi shine zai rage sace-sace, da faɗan daba da sauran muggan Laifuka da suka addabi ƙasar.
Ya kuma yi kira ga malaman addinai daban-daban da suma suji tsoron Allah suke faɗawa shugabanni gaskiya tare da jawo hankalin su da su tabbatar da bada cikakken tsaro a cikin kasar dama jihohi domin rage yawaitar sacewa da kashe al’umma da ake yi.
