News
Shugaba Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Sakin Yaran Da Aka Kama Yayin Zanga Zanga
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin sakin kafatanin kananan yaran da aka kama tare da tsare su lokacin zanga-zanga.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin Najeriya dake Abuja.
Najeriya Ce Kasa Ta 5 Cikin Manyan Kasashen Da Suka Fi Amfani Da Kafafan Sada Zumunta A Duniya
Idris ya ce shugaban Tinubu ya umurci babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, da ya gaggauta fara aikin ganin an sallami yaran.
Advertisements
