News
Najeriya Ce Kasa Ta 5 Cikin Manyan Kasashen Da Suka Fi Amfani Da Kafafan Sada Zumunta A Duniya
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wasu bayanai da aka tattara sun bayyana cewa Najeriya ce kasa ta 5 cikin jerin manyan kasashen dake kan gaba wajen amfani da kafafen sada zumunta na zamani a fadin Duniya.
Bayanan da kamfananin Cable.com.uk da kuma We are Social suka fitar a shekarar nan, kuma hukumar kididdiga ta Duniya ta wallafa a shafin X sun ce a kullum yan Najeriya na shafe akalla sa’o’I 3 da mintuna 23 a kan shafukan sada zumunta.
Sauran kasashen dake sahun gaba wajen amfani da kafofin na sada zumunta sune Kenya, Afrika ta kudu, Brazil da kuma Philippines.
Sai dai duk kasashen 4 sun dara Najeriya ne da yan dakiku a fannin amfani da kafofin na sada zumunta.
Advertisements
