News
Cin Fuska Ne A Wajena Yadda Ake Faɗin “Abba Tsaya Da Ƙafar Ka” – Gwamnan Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce cin fuska ne a wajena kalmar “Abba Tsaya Da Kafarka” kamar yanda wasu suke Faɗa
Abba ya ce shekaru 40 nayi da Kwankwaso na kwashe tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Kuma Muna Tare Dashi har yanzu
Da Dumi-Dumi: Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya ya rasu
Ina mamakin yadda wasu suke cewa na Tsaya da Kafata Kuma wanna Cin Fuska ne gare ni, domin kuwa Kwankwaso Mai gidana ne Muna zaune Lafiya dashi Dan Haka Babu Wata Baraka a tsakaninmu
Daga Yau Laraba 6-11-2024 Duk Wani jami’in Gwamnati ko abokan Arziki ko masoya na haramata masa Kara Cewa na Tsaya da Kafata
Kwankwaso shine Jagoran mu Kuma shine Shugaban mu, Anna Saboda San zuciyar Wasu Suke Kokarin Kawo Mana rikici a Jam’iyyar NNPP Dan Haka nake Muku rantsuwa da Cewa wallahi bani da masaniya akan abinda Wasu Ke Cewa wai Akwai rigima tsakanina da Kwankwaso.
Nayi niyyar zuwa Kotu akan Cewa wai Kwankwaso ya kirani sau 33 ban dauka ba, to Amma na hakura Saboda Yadda nake girmama Yan Jarida acewar Abba Kabir Yusuf Yayin Zanatwarsa da manema Labarai a Daren Laraba a Gidan Gwamnatin Jihar Kano.