News
Da Dumi-Dumi: Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya ya rasu
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da rasuwar Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, babban hafsan sojin kasa.
Lagbaja ya rasu yana da shekaru 56 a duniya.
Tsadar Man Fetur Ta Sanya An Samu Karancin Zirga Zirgar Ababan Hawa A Kano
A cewar wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce ya rasu ne a daren ranar Talata a Legas bayan ya yi fama da rashin lafiya.
“An haifi Laftanar Janar Lagbaja a ranar 28 ga Fabrairu, 1968,
“Babban aikinsa na soja ya fara ne a lokacin da ya shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya a shekarar 1987. A ranar 19 ga Satumba, 1992, aka ba shi mukamin Laftanar na biyu a rundunar sojojin Najeriya a matsayin mamba na kwas na 39 na yau da kullun.
“A tsawon aikinsa, Laftanar Janar Lagbaja ya nuna kyakkyawan jagoranci da jajircewa, inda ya yi aiki a matsayin kwamandan runduna ta 93 da kuma bataliya ta 72 na musamman.
“Ya taka rawar gani sosai a ayyukan tsaron cikin gida da dama da suka hada da Operation ZAKI a jihar Binuwai, Lafiya Dole a Borno, Udoka a Kudu maso Gabashin Najeriya, da Operation Forest Sanity a fadin jihar Kaduna da Neja.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
