News
Tsadar Man Fetur Ta Sanya An Samu Karancin Zirga Zirgar Ababan Hawa A Kano
DAGA AHMAD MUHAMMAD
Tsadar man fetur ta Sanya an samu karancin zirga zirgar ababan Hawa a Arewacin Najeriya musanman a Jihar Kano
Wanda hakan ya jefa da yawan mutane cikin kunci da matsi Inda wasu da dama daga cikin ma’aikatan Gwamnati sun fara tafiyar ƙafa ko bin motocin haya sakamakon tsananin tsadar man fetur.
Dakta Labaran ya Yabi Ƙananan Hukumomin Ajingi, Gaya, Wudil kan Rigakafin Shan-Inna
Ya yin da wasu masu Adaidaita Sahu sun hakura sun ajiye ababan hawannasu sakamakon tsananin tsadar man fetur wanda hakan ne matakin farko da yasanya Adaidaita Sahu yayi tsada kuma yayi karanci.
Jaridar INDA RANKA ta tattauna da wani mutum ya bayyana cewa karancin ababan Hawa ya sanya sukan dade sosai akan titi kafin su samu sukan shafe sama da minti 30 kafin su sami Adaidaita Sahu ya yin da wani lokacin tsada ta kansa wasu su hakura da hawa har Sai sun jira wani koda za su samu sauki.
Haka zalika wani dalibi inda ya bayyana Hakan a matsayin babbar matsala a bangaren tafiyar su makaranta da yawa daga cikin masu Adaidaita Sahu basa San daukar daliban makaranta saboda suna tsammanin cewa ba zasu Iya biyan kudi sosai ba.
Dalibin ya bayyana cewa sukan dade sosai a gefen titi kafin su sami Adaidaita Sahu wasu kuma sukan hakura ne suyi tattaki a kafa ko kuma su nemi ragin hanya a gurin mutanen gari inda wasu sukan taimaka wasu kuma su yi halin ko in kula da su.
Wata ma’aikatciyar Gwamnati amsa tambayar, ta ce yanzu haka ‘yan Najeriya da dama na gyara salon rayuwarsu domin daidaita al’amura, inda aka saba amfani da Motoci wajen zirga-zirgar yau da kullum.
Ta ba da shawarar cewa gwamnati ta ɓullo da motocin bas domin rage wa ma’aikata nauyi da kuma magance matsalolin tsaro a cikin gari.
Ta ƙara da cewa “Mutane da yawa yanzu suna sayar da motocinsu masu amfani da Man Fetur tare da zaɓar wasu samfura masu inganci.”