News
Sabuwar Dokar Yan Adaidaita Sahu Ta Sanya Dalibai Tattaki A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A Larabar nan ne dokar da hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa ta jihar Kano wato KAROTA ta kafa ta hana masu amfani da baburan A daidaita Sahu aiki a wasu manyan tituna ta fara aiki.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa shugaban hukumar KAROTA, Dakta Baffa Babba Dan Agundi na bayyana cewa gwamnati ta samar da motoci da al’ummar jihar zasu dinga hawa manyan titunan da aka hana ‘yan Sahun aiki.
Zargin Tsare Dalibi: Aisha Buhari Ta Kulle Shafinta Na Twitter
Hanyoyin da gwamnatin ta hana ‘yan A daidaita Sahun bi dai sun hada da Titin Ahmadu Bello Way zuwa Gezawa.
A ziyarar da jaridar indaranka ta kai wasu manyan tituna a jihar Kano da safiyar yau ya tarar da tarin dalibai yayin da suke jiran abin hawa a inda ake samun karancin masu baburan na A Daidaita Sahu.
Wakilin namu ya tarar da tarin ‘yan makaranta a titin Hadejia Road suna tattaki a kafa yayin da suke neman abin hawa da zai kaisu makaranta.
Duk da dai Gwamnatin bata hana baburan na Adaidaita Sahu hawa wasu titunan ba sai nan gaba, masu baburan na kaucewa bin wasu manyan hanyoyi a jihar.
Wani ma’aikaci mai suna Abdullahi Tanko ya bayyana mana cewa sai da ya raba babur uku kafin yazo Nassarawa daga Masallacin Sarki.
Sai dai duk da cewa Gwamnatin Kano ta ce ta samar da motocin Taxi 50 da zasu maye gurbin Baburan Dan Sahun har zuwa safiyar yau Laraba basu fara aiki ba.
