News
Mamallakan jiragen alfarma a Najeriya sun maka gwamnati kotu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Masu jiragen sama na kashin kansu a Najeriya sun yanko wa gwamnati sammaci, inda su ke bukatar kotu ta hana ta dakatar da jiragen nasu tashi saboda kin biyan kudin fito.
A watan Nuwamban bara ne hukumar hana fasa kwauri ta kulle jirage 91 mallakar wasu hamshakan masu arziki a kasar, bisa zargin kin biyan kudaden fito da yawansu ya haura naira biliyan 30.
Zargin Tsare Dalibi: Aisha Buhari Ta Kulle Shafinta Na Twitter
Hukumar ta kwastam ta samu sahalewa daga ofishin Shugaban kasa, na umurtar masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama na hana jiragen daidaiku da ake bi bashin kudin fito aiki.
Sai dai jaridar Punch ta cikin gida ta ruwaito cewa mamallakan jiragen na neman kotu ta sake duba halaccin tursasa musu biyan kudin fiton, kamar yadda hukumar kwastam din ke ikirari.
