News
Inganta Lafiya ne Babbar Manufata – Mahmud Tajo Gaya
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A abin da a iya cewa farawa da kafar dama, an bai wa al’ummar ƙaramar hukumar Gaya tabbacin inganta harkar lafiya a yankin yadda ya kamata saboda muhimmancinta ga rayuwar al’umma.
Sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar, Mahmud Tajo Gaya ne ya bayyana haka yayin wata ganawa ta musamman da Sashin Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya lokacin da tawagar duba aikin rigakafin shan-inna da aka kammala kwanan nan ta ziyarci yankin, inda aka yi tattaunawar a ofishin Shirin Rigakafi na Ƙasa (NPI) reshen yankin.
Yan Sanda Za Su Tono Gawar Wata Yarinya Mai Shekara Biyu Da Ake Zargin An Kashe
Tajo Gaya ya ce yana da sha’awa game da lafiya kasancewar tun asali shi ma’aikacin lafiya ne, kuma tsohon Babban mai Taimaka wa Gwamna na Musamman a kan Asibitin Tafi da Gidanka, da ake duba mutane a faɗin jihar Kano da ba su magani kyauta musamman a wurare masu nisa da wahalar shiga.
Ya ce ya tsotsi sha’awar inganta lafiya ne daga wajen Gwamnan lafiya, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan Lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusuf, da hakan ya tsima shi bayan an zaɓe shi ya ƙudiri aniyar inganta fannin lafiya na ƙaramar hukumar Gaya ta hanyar bijiro da hanyoyi daban-daban domin sauƙaƙa wa al’ummarsa.
“Tun da na shiga ofis ban huta ba. Na ziyarci cibiyoyin lafiya na yankin don ganin yadda abubuwa ke tafiya. Nan da nan na ba da umarnin ɗaga likkafar asibitoci biyar su rinƙa yin aiki cikin awanni 24. Zan ci gaba da tallafa wa duk wani shiri da zai taimaki al’ummarmu. Babban abin da na sa a gaba shi ne, inganta lafiya, lafiya, lafiya.
“Lokacin na na zo na tarar akwai cutar kwalara nan da can a wasu sassa na ƙaramar hukumar da ta shafi kimanin mutane hamsin kwance a asibitoci. Mun kula da su har aka sallame su, sannan na bai wa kowane daga cikinsu Naira 10,000,” ya bayyana.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce yana da shirin inganta ƙwarewa da ilimin ma’aikatan lafiya domin a ƙara musu karsashi ta yadda za su yi abin da ya kamata, ya ƙara da cewa abin da yake so daga gare su shi ne su zama masu gaskiya da riƙon amana yayin gudanar da aikinsu domin a inganta tsarin lafiya a ƙaramar hukumar.
Ya nuna gamsuwa da yadda ya samu sashin da sadaukarwar da ma’aikatan lafiya ke nunawa yayin da suke gudanar da ayyukansu a cibiyoyin lafiya daban-daban, ya hore su da su riɓanya kokari domin al’ummar ƙaramar hukumar su amfana sosai.
Tajo Gaya ya ce ya zauna da ma’aikatan sashin lafiyar inda ya yabe su a inda suka yi bajinta tare da yi musu gyara a inda yake ganin akwai buƙatar haka, kuma suka amince, yana mai nuna farin ciki da gudunmawar da ƙungiyoyi masu tallafa wa lafiya ke bayarwa a yankin.
Ya gode wa al’ummar ƙaramar hukumar bisa goyon bayan da suke ba shi tun lokacin da ya zo tare da yin kira gare su da su ci gaba da mara wa manufofi da tsare-tsaren da ya zo da su na ciyar da karamar hukumar gaba baya, yana mai tabbatar musu da shimfiɗa ingantaccen shugabanci.