Connect with us

News

Yadda Kanawa Suka Fara Jingine Motocinsu Suna Rungumar Babur Mai Caji Da Tafiyar Ƙafa Saboda Tsadar Man Fetur

Published

on

Yadda Ƙarin farashin man fetur ke tilasta Kanawa yin tafiyar ƙafa

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Wasu mazauna Kano sun fara jingine motocinsu suna rungumar kekuna da babura masu caji inda wasu ma ke zaɓar tafiyar ƙafa saboda tsadar man fetur da  yanzu ya kai N1,050.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya rawaito yadda a ranar Lahadi a aka yi fama da ƙarancin motoci a kan titi da kuma ƙaruwar mutanen da ake amfani da kekuna da babura masu caji har ma da masu tafiyar ƙasa.

Inganta Lafiya ne Babbar Manufata  – Mahmud Tajo Gaya

Ɗaya daga cikin masu tafiyar ƙasa, Sani Isa, ya bayyanana wa kamfanin dillancin labarai na NAN cewa an samu ƙaruwar kuɗin abin hawa domin masu adaidaida Shahu sun ninka kuɗin da ake biya saboda farashin man fetur.

Ya ce wannan hali da ake ciki ya shafe shi sosai saboda a yanzu Naira 1,200 yake biyan ‘masu abin hawa.

Isa ya ce daga nan ne ya dawo amfani da keke saboda ya fi sauƙi.

Advertisement

Shi ma wani ɗalibi, Aminu Ishaq, wanda ke ke amfani da kekensa zuwa makaranta Fasaha ta Kano, ya ce hatta iyayensa suna amfani da keke saboda tsadar man fetur.

“Ba na ɓata lokacin wajen jiran Adaidaita. A kodayaushe naman ina zuwa makaranta a kan lokaci. Ina jin ƙarfi a jikina” a cewar Ishaq.

Muhammad Sadiq, ma’akmacin gwmnati ne, ya ce a yanzu yana raba tafiyarsa gida biyu, rabi ya yi ta a kafa, rabi kuma ya hau abin hawa wanda hakan ya sa yake samun saukin N300.

“Tun bayan ƙara farashin mai, akwai masu adaidaitar da suka jingine abin hawansu suka canja sana’a,” a cewarsa.

Shi ma Ali Abdullahi , ya ce tun bayan ƙara kuɗin man fetur ya jingine abin hawansa tare da fara amfani da babur mai caji wanda ya rage masa kuɗin da yake kashewa.

Har’ila yau, wani ɗan kasuwa, Tasi’u Murtala, wanda ya sayi babur mai caji kwanan baya, ya ce a da Naira dubu biyar yake kashe wa motarsa.

Advertisement

A cewarsa, ya sayi babur mai caji ne a kan Naira 750, 000 wanda ke taimaka masa wajen rage kuɗin da yake kashewa.

“Idan ka caja babur ɗin ya cika, yana iya tafiyar kilomita 60 kafin cajinsa ya ƙare.

Yana amfani da wuta ko sola ko janareta wajen yi masa caji a kullum,” mutumin ya bayyana.

 

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending