Connect with us

News

Shugabannin ƙungiyar ƙasashen G20 sun hallara a kasar Brazil

Published

on

IMG 20241118 WA0046

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Shugabannin ƙungiyar ƙasashen G20 sun hallara a Brazil a yau Litinin don tattaunawa kan batun yaƙi da talauci da bunkasa hanyoyin tara kuɗaɗen yaki da matsalar sauyin yanayi da sauran tsare-tsare na bangarori daban-daban.

Advertisement

Arzikin duniya, su ne su ke ba da kaso mafi tsoka na kuɗaɗen yaƙi da gurɓatar muhalli, kuma babu ƙasar da ta kai su fitar da hayaƙi mai gurbata muhalli a duniya.

Gwamnoni Na Barazanar Hana Mu Takara A 2027 Matukar Muka Goyi Bayan Dokar Haraji Ta Shugaba Tinubu —Majalisar wakilai

A yayin taron yanayi na COP29, babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce dole ne kowace ƙasa ta bada gudummawa a wannan yaƙi, amma kuma don ƙasashen G20 su kasance a kan gaba, duba da cewa su ne saka fi gudanar da ayyukan da ke gurɓata muhalli.

Advertisement

 

Wannan ne dai karo na ƙarshe da shugaba Joe Biden na Amurka zai halarci taron na ƙasashe masu karfin tattalin arziki, duk da cewa shugaba Xi Jinping na China wanda ya naɗa kansa a matsayin mai ƙarfin faɗa aji a duniya, kuma mai rajin kare ƴancin ciniki daga ƙudurorin Trump ne zai kasance tauraro a wajen taron.

Advertisement

An dai tsaurara matakan tsaro a harabar taron, wanda ke zuwa kwanaki kadan bayan da aka yi yunkurin tada bom a kotun ƙolin ƙasar da ake zargin masu tsatsauran ra’ayi da kitsa hakan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending