News
Yadda Ƙananan Yara Suka Gudanar Da Zama A Majalisar Dokokin Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kananan yara a Kano sun gudanar da zama na musamman a Majalisar Dokokin Jihar Kano na tsawon sa’a daya da rabin don tunawa da Ranar Yara ta Duniya da kuma kira ga inganta tsaro a makarantun jihar.
Yaran, da aka zaɓo daga makarantu daban-daban a fadin jihar, sun wakilci mambobi 40 na majalisar, tare da jagorancin kakakin yara, Mohammed Isa mai shekaru 15.
Yadda Ƙananan Yara Suka Gudanar Da Zama A Majalisar Dokokin Kano
A yayin zaman na musamman da aka gudanar a ranar Laraba, yaran sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta samar da isasshen tsaro a dukkan makarantun Jihar.
Da take gabatar da kudiri a zauren majalisar, Nafisa Sale, mai wakiltar mazabar Rano, ta bayyana cewa tabarbarewar tsaro na tasiri sosai ga yawan yaran da ke ci gaba da karatu da kammalawa, musamman a yankunan karkara.
Ta ce mafi yawan makarantun da ke yankunan sun kasance a rufe saboda barazanar sace-sace da hare-haren da ake kai wa makarantu, wanda ke dagula tsarin karatu.
Haka zalika, kafin wannan, yaran sun ziyarci Sarkin Kano na 16, Malam Mohammed Sanusi, inda suka bayyana matsalolin yara a jihar. Matsalolin sun haɗa da yawan yara marasa zuwa makaranta, shaye-shaye, mutuwar mata a yayin haihuwa, da rashin kula da marayu da zawarawa a al’umma.
A martaninsa, Sarkin Sanusi ya yi alkawarin nemo hanyoyin magance matsalolin yaran tare da kira ga masu ruwa da tsaki a jihar da su yi aiki don shawo kan matsalolin.
Ya kuma yi kira ga yaran da su dage da karatunsu domin zama manyan shugabanni a nan gaba.
A nasa bangaren, jami’in hulda da jama’a na UNICEF a ofishin Kano, Mista Samuel Kalau, ya bayyana cewa Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 20 ga watan Nuwamba don tunawa da yara, ba su damar bayyana ra’ayoyinsu, tare dayin kira ga daukar mataki
