Connect with us

News

Sojojin Mali Sun Tsige Firaministan Kasar Daga Mukaminsa

Published

on

Sojojin Mali sun tsige firaministan kasar daga mukaminsa

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Shugaban mulkin sojan Mali ya kori Firaministan farar hula Choguel Kokalla Maiga da gwamnatin kasar, kwanaki bayan Choguel Kokalla Maiga ya fitar da wata suka da ba kasafai ba kan majalisar sojin kasar ta Mali.

Kasar Mali mai fama da rikicin kungiyoyin masu da’awar jihadi da ‘yan aware, sojoji sun karbi iko tun bayan juyin mulkin da aka yi a shekara ta 2020 da 2021. Choguel Kokalla Maiga, wanda sojoji suka nada bayan juyin mulki na biyu, ya kasance wani mutum da ake kalo a matsayin mai kima aidanun yan kasar ganin ta yada ya soki lamirin manyan kasashen Duniya da ke kokarin ci gaba da mulki bawa da ubangida,sai ga shi ranar Laraba Choguel Kokalla Maiga ya furta wasu kalamai da suka janyo suka daga ciki da wajen kasar musaman ga masu goyon bayan sojoji. Babban sakataren fadar shugaban kasa, Alfousseyni Diawara, ne ya karanta sanarwar sallamar Choguel Kokalla Maiga da gwamnati a gidan talabijin na kasar ORTM.

Advertisement

An Kama Wata Mata Mai Shekara 40 Da Matasa 4 Da Laifin Fashi Da Makami

Wasu jiga-jigan gwamnatin mulkin soja irinsu ministan tsaro Janar Sadio Camara da ministan sulhunta Janar Ismael Wague na cikin gwamnati. A watan Yunin 2022, gwamnatin mulkin sojan ta yi alkawarin shirya zabe tare da mika mulki ga farar hula a karshen watan Maris din 2024, amma daga baya ta dage zaben har abada.

Tsohon Firaministan Mali Choguel Kokalla Maiga a ranar Asabar ya fito fili ya yi Allah-wadai da rashin fayyace game da kawo karshen mulkin farar hula. Ya ce rudanin na iya haifar da “mummunan kalubale da kuma hadarin komawa baya”. Maiga, mai shekaru 66, ya taba rike mukamin minista a lokuta da dama kuma ya tsaya takara sau uku a matsayin dan takarar shugaban kasa. Ya kasance fuskar farar hula na ginshiƙin dabarun mulkin soja daga tsohuwar mulkin mallaka na Faransa da kuma kusancin dangantakar siyasa da soja da Rasha.

Advertisement

A Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumbar 2021, Maiga ya yi tir da abin da ya kira “watse a tsakiyar iska” dangane da sanarwar janye dakarun Faransa da ke yaki da masu da’awar jihadi.

Choguel Kokalla Maiga ya ce janyewar ta tilastawa kasar Mali ta binciko sabbin hanyoyi da sauran kawayenta, a daidai lokacin da kungiyar Wagner ta Rasha ta shiga cikin mawuyacin hali.

Advertisement

 

 

Advertisement

FRI HAUSA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending