News
An Kama Wata Mata Mai Shekara 40 Da Matasa 4 Da Laifin Fashi Da Makami
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Yan sanda a jihar Bauchi sun kama wata mata, Maryam Salisu, mai shekaru 40 tare da wasu matasa hudu bisa zargin su da hannu a laifin fashi da makami da hada baki domin aikata miyagun laifuka.
Matasan hudu da aka kama sune kamar haka; Musa Umar, mai shekara 17, Ibrahim Mohammed, mai shekara 17, Bilal Musa, mai shekara 17, da Idris Jibrim, shi ma mai shekara 17.
Sakacin Da Mutane Ke Yi Ne Ke Haddasa Gobara A Lokacin Sanyi —Hukumar Kashe Gobara
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, shine ya bayyana hakana a wani jawabi da ya rabawa manema labarai ranar Talata a garin Bauchi.
Ya bayyana cewa an kama ma su laifin ne bayan samun bayanan sirri a kan zargin su da aikata miyagun laifuka.
“Yayin samamen da jami’an mu suka kai, sun samu nasarar samun su da na’ura mai kwakwalwa guda biyu, wayar hannu guda hudu, cocilan guda biyu, cajar waya guda uku, da sauran su,” a cewar Wakili.
A cewar Kakakin, rundunar ‘yan sanda ta na gudanar da bincike domin gano alakar wadanda aka kama din da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda da aiyukan ta’addanci.
SP Wakil ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda a shirye ta ke domin tabbatar da tsaro da kuma adalci ga kowa.
