News
Ƙananan Yaran Nan Guda Huɗu ’Yan Gida Ɗaya Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna Sun Kuɓuta.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƙananan yaran nan guda huɗu ’yan gida ɗaya da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna sun kuɓuta.
A daren ranar Litinin ɗin nan aka damƙa yaran su huɗu ga iyayensu baya Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Sha’anin Tsaro ya taimaka wajen ceto su daga hannun masu garkuwa da su.
An fara yajin aiki a wasu jihohin 5 game da mafi ƙarancin albashi
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya raka iyayen yaran zuwa Abuja, inda aka damka musu ’ya’yan nasu mata uku da namiji ɗaya bayan an ceto su.
Mashawarcin Shugaban Ƙasa na Tsaro, Nuhu Ribadu, ya mika yaran, waɗanda daya daga cikinsu marainiya ce.
Yaran masu shekaru biyu da tara da 12 da kuma 14 an sace su ne a gidansu a daren ranar Talata da ta gabata Kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito
An yi abin gaba da su ne a yayin da mahaifunsu ya je dubiyar mahaifiyarsu da ke jinyar ƙannensu tagwaye a asibiti.
