News
Shugaba Tinubu Ya Bayyana Makomar TETFUND Da NITDA Da NASENI
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ɗaya daga cikin masu taimaka wa shugaban ƙasa, Bola Tinubu, kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya tabbatar da cewa babu wani shiri na da ke ƙunshe cikin ƙudurin dokokin sake fasalin haraji na yunƙurin rushe hukumomin gwamnati kamar su, TETFUND (Asusun tallafa wa manyan makarantu) da NITDA (cibiyar bunƙasa ilimin fasahar sadarwa ta zamani) ba. Sai dai za a canja tsarin da ake bi wajen ɗaukar nauyinsu.
Onanuga ya bayyana hakan ne a ranar Litinin inda ya ce ƙudurin dokokin, saɓanin yadda masu fashin baƙi da hasashe ke faɗa, babu wata niyya ta fifita wani ɓangare na ƙasar nan ba.
“Saɓanin shaci faɗin da ake yi cewa nan da shekara ta 2029 bayan ƙaddamar da dokar sake fasalin haraji, za a rushe hukumomin gwamnatin kamar su NASENI da TETFUND da NITDA, waɗannan hukumomi za su cigaba da kasancewa,” in ji Onanuga.
“Ire-iren waɗannan hukumomin gwamnati (NASENI da TETFUND da NITDA) na ware kuɗin ayyukansu ne daga kasafin kuɗin harajin kamfanoni waɗanda ake maganar an tula musu haraji.”
Cibiyar NASENI, cibiya ce ta gwamnatin tarayya da aka kafa ta domin ɗabbaƙa ilimin kimiyya da fasaha a Najeriya. TETFUND kuwa, asusun gwamnatin tarayya ne na musamman wanda muhimmin aikinsa shi ne tallafa wa manyan makarantu da ke faɗin Najeriya, sai kuma NITDA wacce aka ƙirƙire ta domin bunƙasa fasahar sadarwa ta zamani a Najeriya. Kuma dukkansu ana ɗaukar nauyinsu ne da kuɗin harajin da ake ɗora wa sana’o’i.
Onanuga ya ce babban ƙudurin sake fasalin haraji shi ne cure harajojin wuri guda sannan a raba su kamar yadda ya kamata.
“A daɗe ana samun ƙorafe-ƙorafe daga masu zuba hannun jari da kamfanoni masu zaman kansu a Najeriya waɗanda ke kokawa da jibga musu harajojin daban-daban haɗi da waɗanda ake ɗora musu domin ɗaukar nauyin irin waɗancan hukumin gwamnati.
“A sashe na 59(3) na dokar harajin da za a yi, ta ƙunshe ƙoƙarin cure dukkan nau’o’in harajojin da ake ɗora wa kamfanoni waje guda ta hanyar maye gurbinsu da haraji guda ɗaya wanda za a riƙa raba su har da waɗancan hukumomin gwamnati na musamman har zuwa 2030.
“An ɗebar musu tsawon lokaci ne domin ba su damar gano wasu hanyoyin samun kuɗi a karan kansu domin ƙarawa da na kasafin da ake bas su.”
Game Da Ƙudurin Dokokin:
PREMIUM TIMES dai ta bayyana muku yadda waɗannan ƙudurin dokoki suka sha suka daga al’umma a faɗin Najeriya.
ƙudurorin su ne:
Ƙudurin Samar Hukumar Haraji na Haɗin Guiwa ta 2024.
Ƙudurin samar da haraji na Najeriya ta 2024
Kudurin samar da hukumar kula da haraji ta ƙasa
Ƙudurin Sake Fasalin Haraji ta 2024.
Da dama daga cikin ‘yan Najeriya sun soki wannan ƙuduri inda suka riƙa bayyana aniyar ƙudurin dokokin na fifita wasu sassan ƙasar nan, Sai dai masu mara wa ƙudurin dokokin baya sun ce masu sukar ƙudurin ba su ma karanta su ba. Kawai suna yaɗa jita-jita ne.
Ƙudurin dokokin dai sun tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa kuma an miƙa su ga kwamitin majalisar mai kuɗi da sha’anin kuɗi domin gudanar da jin ra’ayin jama’a wanda izuwa yanzu ba kai ga yi ba.
Sanna har zuwa yanzu, majalisar wakilai ba ta gudanar da nata muharar ba a kan waɗannan ƙudurin dokokin.
Muhimman Batutuwa da Onanuga ya yi cikin kalamansa kai tsaye:
Tun bayan fara bayyana ra’ayoyi da al’umma suke yi a makon da ya gabata, ake samun wasu daga cikin ‘yan siyasa da masu fashin baƙi da ke ƙoƙarin jirkitar da gaskiya da kuma karkatar da tunanin al’umma.
Abin takaicin shi ne yadda mafi yawa daga cikin abubuwan da ke faɗa ba gaskiya be ne kuma masu faɗar ba su da cikakken ilimi game da ƙudurorin inda wasu kuma ke ƙoƙarin haɗa al’umma da ‘yan majalisun tarayya ko kuma maishe da abin ɓangaranci.
Ƙudurin dokokin ba zai maishe a Legas ko Ribas mafiya arziƙi ba a Najeriya sama da sauran jihohin ƙasar nan. Ƙudurin ba zai talauta kowacce jiha ba, sai ma alfanu da al’umma za su samu wanda zai inganta rayuwarsu a ƙoƙarin da suke na samun abin kai wa bakin salati.
Nau’in harajin daban-daban da ake da su barazana ce ga yanayin tattalin arziƙin Najeriya wanda ke sa ta rasa masu zuba hannayen jari da hana wasu daga cikin sana’o’inmu bunƙasa ko ɗorewa. Wasu kamfanonin sun yanke shawarar barin ƙasar nan. Ba yadda za a yi mu cigaba da tafiya a haka har nan da shekaru 20 matuƙar dai muna so mu sauke nauyin kawo wa al’umma cigaba.
Gwamnatin tarayya na son kawo ƙarshen nau’o’in haraji ne kama daga harajin kuɗin shiga na ɗaiɗaikun mutane da harajin siyayayya da sauran nau’ikan haraji zuwa ga ɓangaren da ya fi muhimmanci. Sanya haraji domin ɗaukar nauyin wasu hukumomin gwamnati na musamman wanda har yanzu bai kai ga cimma bunƙasar da ake fata ba, abu ne da kudurin dokokin nan ke son kawo ƙarshen su.
Akwai buƙatar shugabanni da al’umma ke kallo da neman jin ta bakinsu a wannan lokaci su fahimci muhimmancin sanin abin da za su faɗa game da muhimman abubuwa kamar na sake fasalin haraji domin kaucewa siyasantar da shi da kuma shigo da ɓangaranci.
Shugaba Tinubu yana maraba da jin ra’ayoyin al’ummar ƙasar nan kama daga jagorori da suka haɗa da gwamnoni da sarakuna da ƙungiyoyin fararen hula da ɗalibai da ƙungiyoyin’yan kasuwa da ƙwararru da sauran talakawa ta hanyar amfani da jin ra’ayin jama’a da majalisun ƙasar nan za su shirya.
