Connect with us

News

Kano Na Bukatar Litar Ruwa Miliyan 700 Domin Biyan Bukatun Yau Da Kullum  

Published

on

Kano Na Bukatar Litar Ruwa Miliyan 700 Domin Biyan Bukatun Yau Da Kullum

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano, Injiniya Garba Ahmad Bichi, ya bayyana cewa jihar na bukatar kusan litar Ruwa miliyan 700 domin biyan bukatun  yau da kullum.

Advertisement

Jaridar KANO FOCUS ta ruwaito cewa Injiniya Bichi ya bayyana haka a ranar Litinin, yayin  kare kasafin kudin hukumar a ginin Majalisar Dokokin Jihar.

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Makomar TETFUND Da NITDA Da NASENI

A cewarsa, hukumar tana da bukatar karin kayayyakin aiki  da kuma rashin isassun famfo.

Advertisement

Sai dai ya lura cewa Gwamnan Jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da siyan karin wasu  famfo domin tabbatar da samun ruwa a jihar.

“Da zarar an kawo su, za a sami babban sauyi, kuma ruwa zai wadatu,” in ji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending