News
Shugaban Kasar Koriya Ta Kudu Ya Kafa Dokar Ta-baci

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Masu zanga-zanga sun mamaye majalisar dokokin Koriya ta Kudu bayan Shugaba Yoon Suk Yeol ya kafa dokar ta-baci. An shiga yanayin rudani bayan shugaban kasar ya kafa dokar ta-bacin.
Shugaba Yoon Suk Yeol na kasar Koriya ta Kudu ya kafa dokar ta-baci lokacin wani jawabi da ya gabatar kai tsaye ta kafofin yada labarai a wannan Talata.
Kano Na Bukatar Litar Ruwa Miliyan 700 Domin Biyan Bukatun Yau Da Kullum
Shugaban ya zargi ‘yan adawa da suka mamaye majalisar dokokin kasar yin sako-sako game da batun kasar Koriya ta Arewa duk da yadda take zama barazanar tsaro ga kasarsa.
Shugaban ya ce ya kafa dokar ta-bacin domin domin magance ‘yan kanzagin Koriya ta Arewa da tabbatar da kundin tsarin mulkin kasar game da ‘yancin fadin albarkacin baki.
Tuni jagoran ‘yan adawa na kasar Lee Jae Myung ya matakin shugaban kasar a matsayin abin da ya saba kundin tsarin mulki. A daya bangararen majalisar dokokin kasar ta kada kuri’an watsi da matakin kafa dokar ta-bacin abin da ya jefa kasar ta Koriya ta Kudu cikin wani sabon rikicin siyasa.