Connect with us

News

Gwamnati Za Ta Fara Yi Wa Yara Allurar Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro

Published

on

Gwamnati za a fara yi wa mutane allurar rigakafin zazzabin cizon sauro

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Hukumar Kula da Cibiyoyin Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta Kasa NPHCDA ta bayyana cewa gwamnati za ta fara yi wa yara allurar rigakafin zazzabin cizon sauro a jihohin Kebbi da Bayelsa daga ranar biyu ga Disamba.

Advertisement

Yin hakan na daga cikin matakan da gwamnati ta dauka domin gamawa da cutar dake yaduwa kamar wutar daji take  kashe mutane a kasar nan.

Shugaban Kasar Koriya Ta Kudu Ya Kafa Dokar Ta-baci

Shugaban hukumar NPHCDA Muyi Aina ya sanar da haka wa manema labarai a Abuja.

Advertisement

Aina ya ce za a yi wa yara kanana ‘yan kasa da shekara biyar allurar rigakafin kyauta a wadannan jihohi.

Ya ce ma’aikatan lafiya za su rika bin mutane gida-gida, asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko dake wadannan jihohin domin yi wa yara rigakafin cutar.

Advertisement

Aina ya ce gwamnati na da burin yi wa yara miliyan 1.5 allurar rigakafin cutar a wadannan jihohi.

Ya ce baya ga allurar rigakafin gwamnati za ta hada da sauran matakan dakile yaduwar cutar da suka hada da raba wa mutane gidajen sauro da bada magungunan cutar kyauta.

Advertisement

Aina ya ce gwamnati za ta yi haka ne tare da hadin gwiwar UNICEF da WHO.

“Gwamnati na da burin ganin ta rage yaduwar cutar zuwa kashi 40% a Najeriya nan da 2030.

Advertisement

Shugaban hukumar ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara a wadannan jihohi da su tabbatar sun mika su an yi musu rigakafin.

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending