News
Gwamnan Nasarawa Ya Kori Sakataren Gwamnatin Da Daukacin Kwamishinoni Da Masu Ba Shi Shawara
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya rusa Majalisar Zartarwar Jihar tare da korar Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Muhammad Aliyu-Ubamdoma da kuma dukkanin hadimansa na musamman.
Rahotanni na nuni da cewa Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron gaggawa na musamman da aka gudanar a gidan gwamnati da ke garin Lafia babban birnin jihar a ranar Juma’a.
Ba Mu San Da Zanga Zangar Ba, Kuma Ba Mu Da Hannu A Cikinta —Kungiyoyin Masu Bukata Ta Musamman
Jim kaɗan bayan tafiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shetima wanda ya kai ziyarar aiki ta kwana ɗaya a jihar domin ƙaddamar da wasu ayyuka a cikin jihar.
Wakilinmu ya kuma ruwaito cewa, ana sa ran rushe hadiman Gwamnan zai yi tasiri sosai wajen gudanar da harkokin mulki da aiwatar da manufofin jihar.
Sai dai wani babban jami’in gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa, duk da cewa har yanzu ba a bayyana dalilan da suka haddasa korar ma’aikatan gwamnatin ba, amma ya ce Gwamna Sule ya yi fice wajen yin garambawul ga tsarin tafiyar da harkokin gwamnatin jihar.
Wakilinmu ya kuma ruwaito cewa, a shekarar 2021 Gwamnan Sule ya rusa Majalisar Zartaswar Jihar, saboda buƙatar samar da tsarin gudanar da mulki mai inganci.
