News
Ba Mu San Da Zanga Zangar Ba, Kuma Ba Mu Da Hannu A Cikinta —Kungiyoyin Masu Bukata Ta Musamman
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyoyin masu bukata ta musamman karkashin kungiyar JONAPWD reshen Jihar Kano, sun nisanta kansu daga zanga-zanga tare da taron manema labarai da aka yi a matsayin Kungiyar Hadin Guiwar masu Bukata ta musamman a jihar.
Hadin Guiwar Kungiyoyin PWDs sun samu labarin wannan zanga-zanga da kuma taron manema labarai da wasu mutane suka shirya don matsa lamba ga gwamnatin Jihar Kano Ƙarƙashin Jagorancin Abba Kabir Yusuf kan kafa hukumar kula da masu bukata ta musamman a jihar.
2025 :Baza Mu Dauki Halin Kunnen Uwar Shegu Da Gwamnati Ke Yiwa Muradin Su Ba —Kungiyar ASUU
Muna nisantar kanmu gaba daya daga wannan taron manema labarai da zanga-zangar da aka zargin masu bukata ta musamman sun shirya ba mu san da zanga-zangar ba, kuma ba mu da hannu a cikinta!
Maimakon shirya zanga-zanga, mun zabi amfani da hanyoyin sadarwa na kai-tsaye da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tanada, inda ake sauraron korafe-korafenmu.
Hadin Guiwar Kungiyoyin PWDs da shugabancin JONAPWD suna son jaddada manyan nasarorin da aka samu wajen inganta rayuwar mutanen da ke da bukata ta musamman karkashin jagorancin Mai Girma Abba Kabir Yusuf.
Mun Dogara Da Wadannan Manyan Nasarori:
1. Kafuwar Ofishin Kula Da Al’amuran PWDs:
Dukkan kungiyoyin PWDs an sanya su karkashin Ma’aikatar Harkokin Mata, Yara, da Masu Bukata Ta Musamman, wanda ya bayar da wata hanya kai-tsaye tsakanin gwamnati da PWDs.
2. Tallafin Kai Tsaye Daga Gwamnati:
A cikin kwanaki 100 na farko na mulkinsa, gwamnatin Jihar Kano ta bayar da gagarumin tallafi ga PWDs, wanda ya hada da:
Na’urorin taimako da kayayyakin lafiya musamman ga masu rauni na kashin baya da wadanda ke fama da kuturta.
Kayan abinci da suka hada da buhunan shinkafa 100 mai kilogiram 10 da buhunan masara 100, da kudin sufuri na Naira 50,000 ga kowanne karamar hukuma dake jihar Kano.
Buhunan shinkafa 200 mai kilogiram 25.
Tallafin kudi kai tsaye na Naira 20,000 ga mutane 2,000 masu bukata ta musamman a jihar Kano.
3. Tallafin Ranar Masu Bukata Ta Musamman :
Gwamnati ta tallafa wa bikin Ranar masu bukata ta musamman ta Duniya ta 2024 da kuma Ranar Kariya Ga Mutanen Da Ke Da Rauni Na Kashin Baya na shekarun 2023 da 2024.
Duk da cewa muna goyon bayan kafa hukumar kula da masu bukata ta musamman, muna jaddada cewa Jihar Kano ita ce mafi dacewa da PWDs a Najeriya kuma tana kan hanyar aiwatar da manufofi na ci gaban PWDs.
Muna godiya ga gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Mai Girma Injiniya Abba Kabir Yusuf kan irin karfafa gwiwa da shigar da PWDs a cikin ajandar ci gaban jihar.
Muna kira ga dukkan mambobin Hadin Guiwar Kungiyoyin PWDs na Kano, JONAPWD da jama’a baki daya, su nisanci duk wata zanga-zanga da ake yi da sunan kare hakkokin PWDs a Jihar Kano, domin wannan ba hanyar mu ba ce.
Muna fatan zaman lafiya ga Jihar Kano da Najeriya baki daya.
Sa hannu:
Musa Muhammed Shaga
JONAPWD Chairman, Kano Chapter
Abdulrahman Uba Daushe
Chairman, SPinal Cord Injury Association, Kano
Musa Muhammed Kura
Chairman, National Association for the Blind
Yahaya A. Yahaya
Chairman National Association for Physically Challenge, Kano
Da’u Sa’idu
IDEA Chairman Kano State
Hajiya Mariya
Albino Association, Kano.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
