Sports
Liverpool Ta Barar Da Maki A Hannun Man United A Premier

DAHA YASIR SANI ABDULLAHI
Liverpool da Manchester United sun tashi 2-2 a wasan hamayya a Premier League ranar Lahadi a Anfield.
Tun farko sun je hutun rabin lokaci ba tare da zura ƙwallo ba a raga, sai da suka koma zagaye na biyu ne karawar ta hamayyar ta canja.
United ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Lisandro Martinez, amma minti bakwai tsakani Liverpool mai masaukin baƙi ta farke ta hannun Cody Gakpo.
Mohamed Salah shi ne ya ci wa Liverpool na biyu a bugun fenariti, karo na 13 da ya zura a ragar ƙungiyar Old Trafford a dukkan haduwa.
Daga baya ne United ta farke ta hannun Ahmad Dialo minti 10 tsakani da wadda ɗan kasar Masar ya zura a ragar United.
Karon farko da suka fuskanci juna a wasan farko da shiga sabuwar shekara tun bayan 1989, inda United ta doke Liverpool 3-1 a Old Trafford ranar 1 ga watan Janairu.
United ta kawo karshen wasa takwas da ta yi a Anfield ba tare da nasara ba a bayannan, wadda aka doke karo huɗu da kuma canjaras huɗu.
Ranar 1 ga watan Satumbar 2024, Liverpool ta je ta ci United 3-0 a wasan farko a kakar bana a gasar, inda Luis Diaz ya ci biyu da kuma Mohamed Salah mai ɗaya.
Ƙungiyar da Ruben Amorin ke jan ragama ta kawo karshen wasa huɗu a jere da aka doke ta – wadda ta fara da rashin nasara a hannun Tottenham da Bournemouth da Wolverhampton da kuma Newcastle United.
Shi kuwa mai horar da Liverpool ya kasa kafa tarihin doke United gida da waje a kakar farko da yake jan ragama – mai rike da bajintar shi ne George Kay a 1936/37.
Tun bayan da Nottingham Forest ta je ta yi nasara a kan Liverpool ranar 14 ga watan Satumbar 2024, daga nan ƙungiyar Anfield ta yi wasa 24 a jere ba tara da rashin nasara ba a dukkan fafatawa.
Da wannan sakamakon Liverpool ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 46 mai ƙwantan wasa.
Ita kuwa United mai maki 23 ta yi sama zuwa mataki na 13 daga gurbinta na 14, bayan buga wasan mako na 20.
Ranar Laraba Liverpool za ta je gidan Tottenham a karawar League Cup daga nan ta karɓi bakuncin Accrington ranar Asabar 11 ga watan Janairu a FA Cup.
United kuwa za ta fafata da Arsenal a Emirates a FA Cup ranar Asabar 12 ga watan Janairu daga nan ta kara da Southampton a Old Trafford ranar Alhamis 16 ga Janairu a Premier League.