Sports
Barcelona Ta Yi Wa Real Madrid Wankin Babban Bargo Tare Da Lashe Kofin Super Cup

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Barcelona ta lashe Gasar Spanish Super Cup na bana bayan ta samu nasara mai ban mamaki da ci 5-2 kan Real Madrid, a ranar Lahadi.
Kylian Mbappé ne ya fara ci wa Real Madrid kwallo tun a minti na 5.
SERAP Ta Maka Shugaba Tinubu Da Gwamnoni A Kotun ECOWAS Bisa Zargin Tauye Hakkunan ‘Yan Nageriya
Amma Barça ta dawo da karfin gaske don juya wasan a nasu bangaren.
Lamine Yamal ya ci kwallon da ta daidaita wasan a minti na 22 kafin Robert Lewandowski, Raphinha, da Alejandro Balde su ci kwallaye guda uku kafin aje hutun rabin lokaci, suna ba su tazarar ci 4-1.
Raphinha ya kara kwallo ta biyar bayan hutun rabin lokaci, amma abu ya dagule lokacin da mai tsaron gida Wojciech Szczęsny ya samu jan kati saboda laifin da ya yi wa Mbappé a minti na 56.
Rodrygo ya zura kwallo ta biyu daga bugun tazara a minti na 60, amma hakan bai isa ya kawo cikas ga nasarar Barça ba.
Wannan nasara na nufin Barcelona ta lashe Gasar Spanish Super Cup karo na 15 kuma karo na farkotun shekarar 2023.