Sports
Gwamnan Kano Ya Kara Wa Yan Wasan Kano Pillars Yan Kasa da Shekaru 19 Kwarin Gwiwa

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Bayan Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gwangwaje Yan Wasan Kano Pillars (Yan Kasa da Shekaru 19) da tsaleliyar mota da Match Bonus, Yan Wasan sun sami karfin guiwa wajen cimma gagarumar nasara.
A jiya, da misalin lokacin Magriba, Yan Wasan sun tafi Jihar Plateau, inda suka fafata wasa a yau da misalin karfe 2:00 na rana. Alhamdulillah, sun samu nasara mai ban sha’awa, inda suka ci kwallaye 5 rairas ba tare da an ramawa ba.
Gwamnatin Kano Za Ta Rinka Tattaunawa Da Al’umma Kai Tsaye Dan Jin Matsalolin Su
Kyautar mota da tallafi daga Mai Girma Gwamna ya kara musu himma da jajircewa, wanda hakan ya bayyana a nasarorin da suke samu.
A halin yanzu, Yan Wasan suna kan matsayi na farko (1st Position) a Gasar Cin Kofin Matasa (Yan Kasa da Shekaru 19) ta Kasa.
Muna matukar godiya ga Allah bisa wannan cigaba mai albarka, tare da fatan samun karin nasarori a gaba. Allah ya taimaki Jihar Kano da Mai Girma Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf.