Sports
Kevin De Bruyne ya buga wasa na 400 a Man City

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
De Bruyne ya buga wa Manchester City wasa na 400 ranar Asabar a karawar da ta doke West Ham 4-1 a babbar gasa ta firimiyar kasar ingila.
Ɗan kasar Belgium, wanda yake kaka ta 10 a Etihad, ya zama na 15 a jerin waɗanda suka buga wa ƙuniyar karawa 400 ko fiye da hakan.
DA DUMI-DUMI:Gwamnan Kano Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinoni Guda 7
Shi ne kan gaba a yawan lashe kofi a ƙungiyar, inda dan wasan pmai shekara 33 ya ɗauki guda 16.
Cikin kofunan da ya ɗauka sun haɗa da Premier shida da League Cup biyar da FA Cup biyu da kofin zakarun nahiyar turai har da Community Shield biyu.
Haka kuma De Bruyne yana cikin ƴan wasa 19 a City da suka ci mata ƙwallaye 100, wanda yake da 104 a raga kawo yanzu.
Ya kuma bayar da ƙwallo 166 aka zura a raga har da 116 daga ciki a Premier League, wanda ya yi karawa 272 a babbar gasar tamaula ta Ingila.
De Bruyne ya koma City a 2015, wanda ya taka rawar gani da ta kai ƙungiyar har karawar karshe a kofin zakarun nahiyar turai a kakarsa ta farko.
To sai dai kawo yanzu yawan jin rauni ke damun ɗan wasan, wanda ake cewa zai koma taka leda a gasar Saudi Arabia daga