Interview
Ya Kamata Matasa Su Maida Hankali Kan Sana’o’i Da Ayyukan Da Za Su Taimaka Wajen Ci Gabansu Da Al’umma Baki Ɗaya —Santuraki Kupto

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
A ranar Asabar, 10 ga Janairu, 2025, Alhaji Usman Saidu, wanda aka fi sani da Santuraki Kupto, ya gudanar da taro tare da matasa 50 daga dukkanin gundumomin Yamaltu Deba, Jihar Gombe. A yayin wannan taro, Santuraki ya gudanar da rijistar matasan a shirin Facebook Connect, wanda ke ba da damar haɗin kai da ci gaban fasaha a tsakanin matasa.
Haka kuma, ya yi amfani da wannan dama don jan hankalin matasa kan muhimmancin dogaro da kai da neman ilimi, tare da jaddada cewa matasa sune jagororin gobe. Ya yi kira gare su da su maida hankali kan sana’o’i da ayyukan da za su taimaka wajen ci gabansu da al’umma baki ɗaya.
Barcelona Ta Yi Wa Real Madrid Wankin Babban Bargo Tare Da Lashe Kofin Super Cup
Wannan taro ya gudana ne a garin Yamaltu Deba, inda aka nuna damuwa kan tasirin rashin dogaro da kai a tsakanin matasa, tare da bayar da shawarwari kan yadda za a magance matsalolin dake hana su samun cigaba mai ɗorewa.
Mun tabbatar da cewa wannan mataki da Santuraki ya dauka zai taimaka wajen zaburar da matasa su rungumi ci gaba ta hanyar amfani da damar da zamani ya bayar, musamman wajen amfani da hanyoyin sadarwa na zamani kamar Facebook Connect.