Connect with us

News

Likitocin Asibitin Aminu Kano Sun Cire Min Mahaifa Da Jaririna Ba Tare Da Sanina —Maimunat

Published

on

A asibitin Aminu Kano likitoci suka cire min mahaifa da Jaririna ba tare da sanina ba Maimunat Ibrahim da ga Kano

DAGA MAIMUNA RABIU UMAR 

Wata mata mai suna Maimunat Ibrahim  ta ce  likitocin asibitin Aminu Kano sun cire mata  mahaifa da Jaririn ta ba tare da sanina ba

Advertisement

Maimunat ta bayyana hakan ne a shirin yamma na Brekete Family Arewa na ranar Al-hamis ɗin da ta gabata, wanda Human Right Radio Abuja ke gabatarwa.

Tiktok Ya Dawo Aiki A Kasar Amurka Bayan Alkawarin Jirkinta Haramta Shi A Kasar Da Donald Trump Ya Yi 

Mahaifiyar ta ce, “Na kwashe kwana kusan goma a cikin wani ɗaki da likitocin Asibitin suka kaini kafin su cire min mahaifa da jaririn da ke ciki na, kuma dika ba tare da na sani ba” Inji Maimunat

Advertisement

Tinda fari, Maimunat Hamza Ibrahim, wadda ‘yar asalin Kano ce ta ce, wani likita mai suna Dr. Nuhu da wata Dr. Jamila a Asibitin ne suka ce ta kwanta a kan gadon da ake ɗaukar marasa lafiya bayan sun kirawota da Jaka da kuma Wawiya.

Maimunat ta kuma ƙara da cewa, har barazanar sace mata sauran ‘ya’yan da ta haifa akayi bayan ta kaisu ƙara wata hukumar ƙwatar ‘yanci matsawar ba ta daina tuhumar Asbitin na Malam Aminu Kano da sace mata mahaifa da kuma jaririnta ba.

Advertisement

Ta ce sai daga bayan aikuwar lamarin ne, mijinta ya ce ya bunne jaririn da ta haifa lamarin da ya ƙara damula mata lissafi, ace an binne jariri ba tare da kowa ya sani ba.

To sai dai cikin wani saƙo da hukumar gudanarwar Asibitin na Malam Aminu Kano ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ƙaryata wannan zarge-zarg da akayiwa likitocinta, sai dai ta ce duk da haka zata ƙara zurfafa bincike.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending