Connect with us

News

Kotu Ta Yanke Wa Wanda Ya Kashe  Mahaifinsa Hukuncin Daurin Rai Da Rai 

Published

on

Kotu ta yanke wa Muhammad Buba hukuncin daurin rai da rai bisa laifin kashe mahaifinsa

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Wara Babbar kotu dake garin Minna ta yanke wa Abubakar Muhammad-Buba hukuncin daurin rai da rai bayan an kama shi da laifin kashe mahaifinsa.

Kotun ta gurfanar da Abubakar ranar 9 ga Oktoba 2023 bisa laifuka hudu da kisa, sata da sauran su.

Likitocin Asibitin Aminu Kano Sun Cire Min Mahaifa Da Jaririna Ba Tare Da Sanina —Maimunat

Rundunar ‘yan sandan dake Korokpa a kauyen Chanchaga ne suka kama Muhammad-Buba yayin da ya zo karban kudin filin mahaifinsa da ya siyar.

Bisa ga karan da aka shigar a kotun Muhammad-Buba ya caki mahaifinsa da wuka inda baya ya mutu ya yi gunduwa-gunduwa da shi ya zuba jikin a le da sannan ya jefar a kusa da madatsar ruwan Tagwai Dam dake Chanchaga.

Daga nan sai Muhammad-Buba ya je ya sanar da babban amincin mahaifinsa Kuma shugaban kungiyar masu hako na’adanai na jihar Naje Mohammed SD Mambo cewa an yi garkuwa da mahaifinsa Kuma nana bukatan wasu kudade na fansa.

Advertisement

Bayan ya karbi kudin fansan sai Muhammad-Buba ya kara sanar da abokin mahaifin cewa maharan da suka yi garkuwa da mahaifinsa sun sako shi amma mahaifin ya ji rauni kuma yana bukatan fida a asibitin Gwagwalada.

Daga baya dai Mambo ya gano cewa Muhammad-Buba karya yake masa inda hakan ya sa ya sanar da ‘yan sanda.

 

Alkalin kotun Mohammed S.A. Mohammed ya yanke wa Muhammad-Buba hukuncin daurin rai da saboda fannin da suka shigar da kara sun tabbatar wa kotun cewa shine ya kashe mahaifinsa.

Mohammed ya ce bisa ga laifin kisa da Muhammad-Buba ya aikata kamata ya yi a yanke masa hukuncin kisa amma ya yi masa sassauci ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

 

Advertisement

PREMIUM TIMES 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending