News
Tsadar Waken Soya Da Man Girki Na Ci Gaba Da Karya Jarin Masu Sana’ar Awara
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Mafi akasarin masu sana’ar sayar Awara a cikin birnin Kano da kewaye sun daina kasuwanci saboda tsadar kayan hadi.
Kayan hadin sun haɗa da waken soya, man Girki, da kuma makashi, waɗanda farashinsu ya yi tashin gwauron zabi a kwanakin nan.
Kotu Ta Yanke Wanda Ya Kashe Mahaifinsa Hukuncin Daurin Rai Da Rai
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa Awara wani nau’in kayan abinci ne na gida da ake yi daga Waken Soya, kuma ake ci a Arewacin Najeriya, musamman a yankin Arewa maso Yamma.
Binciken da muka yi a wasu wurare daban-dabam waɗanda suka haɗar da kasuwanni da tituna da kuma wasu muhimman wuraren a birnin Kano an gano cewa mutane musamman matasa sun koma sayen Dan Kali saboda yana da arha idan aka kwatanta da Awara.
Bincken ya gano cewa da kuɗin ka N200 ko N300 ya isa karin kumallo ko abincin rana ko ma abincin dare, dangane da bukatar mai saye da kuma lokacin da yake buƙatar.
A yanzu dai ana sayar da waken soya tsakanin Naira 2,200 zuwa Naira 2,300, gwargwadon irin nau’in da ake samu a kasuwa, yayin da man gyada da aka fi , ana sayar da shi tsakanin Naira 2,700 zuwa Naira 2,900. yayin da buhun icce kai N10,000.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
