Connect with us

News

Hukumar Kula Da Aikin Hajji Ta Najeriya Ta Sanar Da Kudin Aikin Hajjin Bana

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar Hajji ta Ƙasa NAHCON ta sanar da kuɗin kujera da kowani maniyyaci zai biya a aikin Hajji na bana.

Wannan sanarwa na ƙunshe ne a sako da ta fito daga hukumar ranar Litinin wanda kakakin hukumar, Fatima Usara ta saka wa hannu.

Tsadar Waken Soya Da Man Girki Na Ci Gaba Da Karya Jarin Masu Sana’ar Awara

Bisa ga sanarwar, maniyyata daga jihar Barno za su biya naira miliyan N8,327,125.59 sai kuma maniyyata daga yankin Arewa za su biya N8, 457,685.59

Maniyyata daga yankin Kudu za su biya N8, 784, 085.59.

Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Usman, ya mika godiyarsa ga wadanda syka yi aikin da ya kai ga aka kai wannan matsayi.

Advertisement

Idan ba a manta ba, baya ga naira miliyan 8 da kowanni maniyyaci ya biya kuɗin kujera a bara, gwamnati ta kara masa naira miliyan 1.6, wanda kuɗi nnlowacce kujera ya kama naira miliyan 9.6.

Tsohon shugaban hukumar, Jalal Arabi, ya bayyana haka a lokacin da yake bayani kan abinda hukumar ta yi da tallafin naira biliyan 90 da gwamnatin Najeriya ta bada.

Arabi ya ce, kudaden da maniyyata suka biya bai isa a iya jigila da ɗawainiya da su ba, dalilin da ya sa ya cika wa kowanni Alhaji naira 1.6 kenan domin a wanye lafiya.

Sai dai duk da waɗannan fashin lissafi da yayi bai gamsar da hukumar EFCC ba, yana nan ana cigaba da tuhumarsa bisa zargin yin sama da faɗi da kuɗaden wasu bangare na wannan tallafi da aka baiwa hukumar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending