Connect with us

News

Ɗalibai Northwest Sun Sauya Murnar Kammala Makarantar Su Zuwa Ziyarar Gidan Gyaran Hali A Kano 

Published

on

IMG 20250124 WA0051

DAGA MAIMUNA RABIU UMAR 

Daliban da suka karanta ilimin kimiyyar bayanai da dakin adana bayanai (Library and Information Science), a Jami’ar Northwest dake Kano suka kammala karatun su.

Toh sai kuma Daliban sun fito da sabon salon bikin kammala makarantar da aka saba gani, inda suka kai ziyara gidan gyaran hali da tarbiyya na gwauron dutse dake jihar kano, domin nuna farin cikin su da kuma godiya ga Allah wanda ya yi musu wannan baiwa.

Babu Jiha Ko Daya A Arewa, Wacce Ke Da Kwararrun Malamai Kashi 50 Cikin 100. – Babangida Aliyu

Ziyara tasu ta gudana ne karkashin jagorancin Kwamared Abdurrashid B. Imam, inda suka tallafa musu da kayan amfanin yau da kullum harma da Tufafin sanya wa a jikin su.

A cewar B. Imam, “Mun dauki matakin kai ziyarar ne domin sauya salon bukukuwan da dalibai suke yi idan sun kammala makaranta na yin anko da kuma daukar Hotuna kawai”.

Haka kuma ya yi kira ga ‘yan uwan sa Dalibai da su yi koyi da irin wannan aikin na Alkhairi, domin ta hakan ne za su fi samun albarkar karatun da kuma ladan da zai taimake su a Lahira.

Advertisement

Bugu da kari Daliban sunyi alkawarin komawa gidan dama sauran gidajen gyaran halin da ke sassan jihar, domin kara tallafa musu da abubuwan da suke bukata, musamman bangaren mata da suke matukar bukatar audugar mata da kunzugun yara.

A karshe shugaban tawagar ya godewa dukkan wadanda suka bada gudummawar su ta kowanne bangare, wanda ya basu damar aiwatar da wannan abin alkhairi

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending