News
Manoman Rani Na Fargabar Ci Gaba Da Asara Sakamakon Karancin Ruwa A Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Manoman Rani a yankin Madatsar Ruwa ta Watari, da ke karamar hukumar Bagwai a Jihar Kano, sun bayyana fargabar fuskantar mummunar asara sakamakon karancin ruwan manoman rani da suka fuskanta fiye da shekaru uku da suka gabata.
Shugaban Kungiyar Manoman yankin, Alhaji Ibrahim Sani Jan-ruwa, ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai, inda ya nuna yadda matsalar ta shafi gonakin yankin.
Babu Wani Mai Ƙarfin Iko Da Ya Isa Ya Tilasta Wa Falasɗinawa Barin Ƙasarsu —Erdogan
A cewarsa, a shekarun baya, Bankin Bunkasa Harkokin Addinin Musulunci na Duniya ya bayar da tallafin kudi domin fadada da kuma gyara hanyoyin ban ruwa a yankin Watari.
Sai dai, ya ce an damka aikin ga wani dan kwangila da ba shi da isassun kayan aiki, wanda hakan ya haifar da aikin da bai da inganci, lamarin da ya janyo koma baya maimakon ci gaba.
Jan-ruwa ya bayyana cewa, a cewar yarjejeniyar, aikin ya kamata a kammala cikin watanni shida. Duk da haka, bayan fiye da shekaru uku, har yanzu ba a kammala shi ba, kuma an yi watsi da shawarwarin manoma, lamarin da ya janyo babbar matsala.
Sakamakon haka, fiye da gonaki dubu 10 sun rasa ruwan da suke amfani da shi, abin da ke zama barazana ga zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin Kano. Ya kara da cewa, a halin yanzu, kaso daya ne kawai cikin kaso hudu na gonakin yankin ke samun ruwan amfani.
Shugaban Kungiyar Manoman ya bukaci hukumomi da kungiyoyin da abin ya shafa da su dauki matakin gaggawa don magance matsalar, domin kaucewa matsanancin karancin abinci da hauhawar rashin aikin yi a Kano da ma kasa baki daya. Ya jaddada cewa, Madatsar Ruwa ta Watari na taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci da ayyukan yia Najeriya.
