News
Mutum 80 Sun Tsallake Rijiya Da Baya A Hadarin Jirgin Sama A Toronto
DAGA MAIMUNA RABIU UMAR
Babban jami’in hukumar kashe gobara na birnin Toronto, Todd Aitken, ya bayyana cewa mutum 18 daga cikin fasinjojin sun samu raunuka a hadarin jirgin da ya taso daga Minneapolis, Amurka, zuwa Kanada.
Mai rikon mukamin Magajin Garin Toronto, Olivia Chow, ta ce ta yi matukar firgita da jin labarin hadarin, amma ta samu kwanciyar hankali bayan tabbatar da cewa dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin – kimanin mutum 80 – sun tsira da ransu. Ta bayyana hakan a shafinta na X.
Wannan hadari ya faru ne a daidai lokacin da ake fama da yawaitar hadurran jiragen sama a arewacin Amurka. A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, wani jirgin helikwafta na soji ya yi taho mu gama da jirgin fasinja a birnin Washington, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 67.
Haka kuma, wani jirgin daukar marasa lafiya ya fadi a Philadelphia, inda mutane bakwai suka rasa ransu, sai kuma wani hadarin jirgin sama a Alaska da ya halaka mutum 10.
Ko da yake ba a rasa rai a hadarin jirgin na Toronto, lamarin ya kara jaddada bukatar tsaurara matakan tsaro a harkokin sufurin jiragen sama.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
