News
Ma’aikatan Hukumar Ruwan Sha A Kano Sun Tsunduma Yajin Aiki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ma’aikatan Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Kano sun tsunduma yajin aiki tare da gudanar da addu’o’in Alqunuti, domin neman saukin halin da suka tsinci kansu a ciki. Wannan mataki ya biyo bayan gazawar Gwamnatin Jihar Kano wajen fara biyansu sabon mafi karancin albashi na Naira 71,000, wanda aka tsara domin inganta rayuwar ma’aikata.
Baya ga haka, ma’aikatan sun koka kan rashin biyan su wasu hakkokinsu na tsawon lokaci, lamarin da suka ce yana hana su jin daɗin aikinsu da gudanar da rayuwarsu yadda ya kamata. Sun bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne domin jawo hankalin mahukunta su gaggauta magance matsalarsu tare da tabbatar da adalci ga dukkan ma’aikata a fadin jihar.
An Kama Mutane 17 A Kano Bisa Zargin Shiryawa Tayar Da Tarzoma
Tuni dai yajin aikin ya shafi ayyukan samar da ruwan sha a Kano, inda jama’a ke fuskantar matsaloli sakamakon dakatar da ayyukan da ma’aikatan suka yi. Ma’aikatan sun jaddada cewa ba za su janye yajin aikin ba har sai an biya su hakkokinsu kamar yadda doka ta tanada.
