News
An Kama Mutane 17 A Kano Bisa Zargin Shiryawa Tayar Da Tarzoma
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da kama matasa 17 da ake zargi da shirya tayar da zaune-tsaye a wasu sassan jihar, wanda ya kai ga rufewar. titin zuwa gidan Gwamnatin Jihar Kano.
Rahotanni na nuni da cewa rundunar, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, ta tura jami’anta domin tabbatar da doka da oda a yayin da ake samun rahotanni game da zanga-zangar da wasu ke shiryawa.
A cikin sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an kama mutanen da ake zargi kuma bincike kan lamarin ya fara.
Rundunar ta tabbatar da cewa za a ci gaba da samar da tsaro don kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da kira ga jama’a da su baiwa hukumomi rahoton duk wani motsi da bai dace ba.
