News
NANS Zata Yi Zanga-zanga Kan Rufe Makarantun Boko A Wasu Jihohin Arewa Saboda Azumin Ramadan
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar Dalibai ta Kasa (NANS) ta bayyana shirin gudanar da zanga-zanga don kalubalantar matakin rufe makarantu a wasu jihohin arewa saboda Azumin Ramadan.
Jihohin da abin ya shafa sun hada da Kano, Bauchi, Kebbi da Katsina, inda gwamnatocin jihohin suka bayar da hutun don saukaka wa al’umma, musamman malamai, wahalhalun Azumin.
NANS ta ce matakin rufe makarantu zai hana dalibai cigaba da karatu, tare da jefa su cikin rashin sanin makomar karatunsu.
Itama Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta yi Allah wadai da wannan mataki, tana mai cewa bai dace a daina karatu saboda Azumi ba, musamman a cikin wata mai muhimmanci kamar watan Ramadan.
Kungiyoyin biyu na kira ga gwamnatocin jihohin da su janye wannan doka domin bai wa dalibai damar cigaba da karatunsu ba tare da katsalandan ba.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
