News
Kwamitin Majalisa Ya Bukaci Dakatar Da Sanata Natasha Na Tsawon Watanni 6
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawa ya bayar da shawarar dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni 6, biyo bayan dambarwar da ta barke tsakaninta da shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio.
Tashar talabijin ta Arise TV ce ta rawaito wannan labari a yau Alhamis.
Ana dai alakanta wannan rikici da zargin da Sanata Natasha ta yi na cewa shugaban majalisar na kokarin yin lalata da ita, zargi da ya janyo cece-kuce a tsakanin bangarorin biyu.
Idan za a iya tunawa, a jiya Laraba wata kotun tarayya dake Abuja ta dakatar da majalisar dattawa daga daukar matakin ladabtawa akan Sanata Natasha, har sai an kammala sauraron karar da ta shigar a gaban kotu.
Har yanzu dai ana jiran jin matsayar majalisar game da wannan shawara da kwamitin ya bayar.
