Connect with us

News

Zalunci Ba Zai Taba Ɗorewa Ba – Sanata Natasha

Published

on

FB IMG 1741274096504

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Ƴar Majalisar Dattawa mai wakiltar Jihar Kogi, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana cewar zalunci ba zai taba ɗorewa ba yayin da take barin zauren Majalisar sakamakon dakatar da ita da aka yi na tsawon watanni shida.

Advertisement

Sanata Natasha ta furta hakan ne bayan Majalisar ta yanke hukuncin dakatar da ita saboda zargin da ta yiwa Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, na cin zarafi da kuma hana ta gudanar da aikinta yadda ya kamata.

Kwamitin Majalisa Ya Bukaci Dakatar Da Sanata Natasha Na Tsawon Watanni 6

Yayin da take barin zauren Majalisar, Sanata Natasha ta kunna na’urar magana inda ta jaddada cewa:

Advertisement

> “Zalunci ba zai taba ɗorewa ba, kuma gaskiya za ta yi halinta ko da tsawon lokaci.”

Majalisar Dattawa ta amince da dakatar da Sanatar na watanni shida tare da buƙatar ta rubuta takardar neman afuwa ga Majalisar. Haka kuma, an bada umarnin rufe ofishinta da hana ta shiga harabar Majalisar har sai dakatarwar ta ƙare.

Advertisement

A cewar Majalisar, jami’an tsaron ta da duk wanda ke aiki da ita suma an dakatar da albashinsu, yayin da aka hana ta wakiltar Najeriya a duk wata tafiya ta ƙasashen waje.

Sanata Natasha ta bar zauren Majalisar da ƙwazo, tana mai jaddada cewa zalunci da danniya ba su da tushe kuma baza su daɗe ba.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending