News
Jami’an NDLEA Sun Harbe Wata Budurwa Mai Shekaru 19 A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jami’an hukumar yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ta NDLEA a Kano sun shiga hannu bayan sun harbe wata budurwa mai shekaru 19, Patience Samuel, a unguwar Jaba.
Wani masani kan tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Alhamis, inda ya ce lamarin ya faru ne da daren Laraba misalin karfe 10:55 na dare.
Jami’an da ake zargi, Nass Ridwan Usman mai shekaru 23 da Sna Ismaila Yakubu mai shekaru 26, na aiki ne a hedikwatar NDLEA ta Jihar Kano.
A cewar rahoton, tawagar ‘yan sanda ta isa wurin da lamarin ya faru, inda suka samu gawar marigayiyar kuma nan take suka garzaya da ita zuwa asibitin koyarwa na Abdullahi Wase. Amma, likitoci sun tabbatar da mutuwarta tun kafin a kai ta asibitin.
Sai dai har yanzu NDLEA ko ‘yansanda ba su fitar da wata sanarwa dangane da lamarin ba.
