News
An Kama Wasu ‘Yan Pakistan Biyu Kan Jagorantar Kungiyar Masu Garkuwa Da Mutane A Legas
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wasu ‘yan kasar Pakistan biyu da ake zargi da jagorantar wata gungun masu garkuwa da mutane da ke aiki a birnin.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya bayyana a ranar Alhamis cewa kamen ya samu ne sakamakon umarnin babban sufeton ‘yan sanda na kasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, wanda ya bukaci daukar mataki mai karfi kan masu aikata miyagun laifuka.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Olohundare Jimoh, ya yaba da kokarin jami’an sashin Ikeja, inda ya ce wannan nasara na nuna jajircewar rundunar wajen kare lafiyar al’umma.
“Za mu ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da cewa Legas ta zama wuri mai aminci ga kowa,” in ji CP Jimoh.
Rundunar ta bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da hadin kai da kuma kai rahoton duk wata barazana da ta shafi miyagun laifuka. Bincike na ci gaba don tabbatar da gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.
