News
Majalisar Wakilai Ta Amince Da Ƙudurorin Sauya Dokar Haraji
Majalisar Wakilan Nijeriya ta amince da kudirin sake fasalin haraji da Shugaba Bola Tinubu ya miƙa wa majalisar dokokin kasar.
A ranar Alhamis ne Majalisar Wakilan ta amince da rahotan ƙudurorin gyara haraji guda hudu a zamanta da ta yi a Abuja, kamar yadda mai taimaka wa Shugaban Ƙasa na Musamman kan Watsa Labarai ya wallafa a shafinsa na X.
A yanzu ana jiran amincewar Majalisar Dattijai ne.
Kudurorin sun hada da dokar harajin Nijeriya da daftarin kula da haraji da dokar hukumar haraji, da kuma dokar kafa hukumar tattara kudaden shiga ta Nijeriya.
Wannan ya biyo bayan nazarin saɗara-saɗara na duk gyare-gyaren da suka dace akan kudurorin a Kwamitin Gabaɗaya.
Wasu daga cikin gyare-gyaren sun haɗa da barin harajin VAT a kan yadda yake a yanzu wato kashi 7.5 cikin 100, sabanin yadda aka so ƙara shi, da kuma tsawaita keɓance harajin kuɗin shiga ga takamaiman kasuwancin noma da jami’an soja.
Tare da amincewa da rahoton kan kudurorin haraji, Majalisar Wakilai na kokarin ganin ta amince da kudirin haraji a mako mai zuwa yadda zai zama doka.
Tsarin raba kuɗaɗen haraji na VAT da majalisar ta amince da shi:
Za a dinga raba kashi 50 cikin 100 daidai wa daida ga jihohin ƙasar
Sai kuma a raba kashi 20 cikin 100 bisa ga yawan jama’ar jihohi
Kashi 30 cikin 100 kuma za a raba shi bisa ga abin da yawan abin da jihohin ke samarwa
Kawar da damuwowin ‘yan Nijeriya
Da yake jawabi bayan majalisar ta yi nazari tare da amincewa da rahotan kudirorin gyara haraji guda hudu, Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Wakilai, James Faleke, ya bayyana cewa an kawar da dukkan damuwar da ‘yan Nijeriya suka nuna a cikin takardun.
Dan majalisar ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa dokar sake fasalin haraji za ta samar da dokokin da za su samu karbuwa sosai.
“An shafe kwanaki uku ana zaman sauraron ra’ayoyin jama’a a kan waɗannan ƙudurorin, tare da gabatar da bayanai daga manyan masu ruwa da tsaki sama da 80. Bayan haka, mun gudanar da ganawa ta kwanaki takwas don yin muhawara a kan kowace saɗara.
“Na yi farin ciki da cewa ‘yan majalisar sun amince da kyakkyawan aikinmu kuma sun amince da duk shawarwarinmu,” in ji Faleke.
Majalisar ta yi gyaran fuska ga batun harajin gado mai cike da cece-kuce, inda ta bayyana cewa duk wani gadon da aka samu kafin rushe batun ba za a iya biya masa haraji ba.
Majalisar ta kuma amince da samar da ci gaba da ba da tallafi ga hukumomin TETFUND, NASENI, da NITDA ta hanyar asusun ci gaba.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News5 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News4 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
