Connect with us

News

Ƙudurin Cire Kariya Ga Gwamnoni Da Mataimakansu Ya Tsallake Karatu Na Biyu

Published

on

image (1)

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da karatu na biyu na wani ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa, gwamnoni da mataimakansu. Wannan mataki na nufin ƙarfafa yaƙi da cin hanci da rashawa tare da tabbatar da gaskiya a tsakanin masu riƙe da muƙaman gwamnati.

Advertisements
Advertisements

A cewar rahotanni, wannan ƙuduri yana cikin jerin gyare-gyare 42 da majalisar ke aiki a kansu, a wani yunƙuri na sake fasalin kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999. Daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna akwai ƙudurin da ke neman raba ofishin Antoni Janar na Tarayya da na Jiha daga ofishin Ministan Shari’a da Kwamishinan Shari’a, da kuma ƙirƙirar sababbin jihohi kamar Ijebu, Ife-Ijesa, Tiga, Orlu, da Etiti.

Advertisements

Tchiani Ya Zama Shugaban Rikon Kwarya Na Nijar Na Tsawon Shekaru 5

Wannan mataki na Majalisar Wakilai na nuna ƙudirin gwamnati na magance matsalolin cin hanci da rashawa, tare da ƙarfafa gaskiya da rikon amana a tsakanin shugabannin ƙasa da jiha. Duk da haka, ƙudurin zai buƙaci amincewar Majalisar Dattawa da rattaba hannu daga Shugaban Ƙasa kafin ya zama doka.

Advertisements
Advertisements
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending