News
Tchiani Ya Zama Shugaban Rikon Kwarya Na Nijar Na Tsawon Shekaru 5
A yau aka gudanar da bikin rantsar da Janar Abdourahamane Tchiani a matsayin shugaban rikon kwarya na Jamhuriyar Nijar na tsawon shekaru biyar. An gudanar da taron ne a wani babban ɗakin taro da ke birnin Yamai, inda manyan ‘yan siyasa suka halarta, ciki har da tsohon shugaban ƙasa, Mahamadou Issoufou.
Advertisements
Advertisements
Baya ga rantsar da shi, an kuma ƙara masa muƙami, inda yanzu ya zama janar mai tauraro biyar, lamarin da ke nuni da ƙarin ƙarfin iko a mulkinsa. Wannan mataki ya janyo cece-kuce, inda wasu ke goyon baya yayin da wasu ke ganin ya saba da yarjejeniyar wucin-gadi da aka yi a baya.
Advertisements
Yanzu dai al’ummar Nijar na dakon yadda gwamnatin rikon kwarya za ta tafiyar da harkokin ƙasa, da kuma ko za a samu sabon shiri na mika mulki ga farar hula a nangaba.
Advertisements
Advertisements
Advertisements
