Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Koka Kan Yadda ’Yan Nijeriya Ke Rage Shan Madara

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwa kan yadda ake kara fuskantar koma baya wajen shan madara a fadin Najeriya, lamarin da ta ce yana barazana ga lafiyar al’umma da ci gaban tattalin arzikin kasa.

Ministan Raya Kiwon Dabbobi, Hon. Idi Mukhtar Maiha, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin bikin Ranar Madara ta Duniya ta shekarar 2025, wanda aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

Advertisement

Indiya Ta Tabbatar Da Asarar Jiragen Yaƙi A Arangamar Da Ta Yi Da Pakistan

Ya bayyana cewa karancin shan madara da kuma rashin wadatuwa da ita a cikin gida na daga cikin manyan kalubale da ke hana bangaren kiwo da sarrafa abinci bunkasa yadda ya kamata a Najeriya.

“Najeriya na bukatar kusan tan miliyan 1.7 na madara a kowace shekara, amma abin takaici, muna iya samar da kimanin tan 600,000 ne kawai a cikin gida – wanda bai wuce kashi 35 cikin dari na bukatar kasa ba,” in ji Ministan.

Advertisement

Ministan ya kara da cewa, “Sauran kashi 65 cikin dari na madarar da ake bukata ana shigo da su ne daga kasashen waje, yawanci a cikin samfurin madarar foda, lamarin da ke lakume sama da dala biliyan 1.5 a duk shekara.”

Ya ce wannan dogaro da kayayyakin waje na rage wa tattalin arzikin Najeriya karfi, tare da hana bunkasar masana’antun cikin gida da kuma lalata damammakin aikin yi a fannin kiwo da sarrafa abinci.

Advertisement

Ranar Madara ta Duniya dai Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ce ta kirkiro da ita a shekarar 2001, kuma ana gudanar da bukukenta a duk shekara ranar 1 ga Yuni domin wayar da kai kan muhimmancin madara ga lafiyar dan Adam da kuma ci gaban bangaren noma mai dorewa.

Gwamnatin tarayya ta yi kira da a kara zuba jari a fannin kiwon dabbobi da sarrafa madara a cikin gida, tare da karfafa gwiwar manoma da masu kiwon shanu domin magance gibin da ake samu a fannin.

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending